Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ana sa bangaren Birgadier Ganaral Qadir Rahimzade kwamandan barikin sojijin sama na Khatamul Anbiya ya fadi cewa: matakin farko na Atisayin hadin guiwar na musamman na tsaron kasa zai kun shi aikewa da sabbin makaman kariya da ke iya mayar da martani daga nesa da kuma tsinakayar duk wani motsi cikin hanzari, da dai sauran dabarun kare kai daga harin abokan gaba,
Daga karshe Birgediya janar Qadir ya fadi cewa a Atiyasan an gudanar da zirga - zirga da jiragen sama na liken Asiri da na marasa matuki da dakarun kare juyi suka kera. Kana ya fadi cewa babban hadafin gudanar da Atisayin shi ne kare muhimman cibiyoyin tsaro da kuma iyakokin kasar .
342/